logo

HAUSA

UNICEF: Fari a sassan Afirka ya sanya yara cikin bala’i

2022-08-24 13:54:59 CMG Hausa

Asusun kula da kananan yara na MDD (UNICEF) ya yi gargadin cewa, yara da dama a yankin kahon Afirka da yankin Sahel, za su iya shekawa barzahu, matukar ba a samar da agajin gaggawa ba, saboda rashin abinci mai gina jiki mai muni da kuma hadarin kamuwa da cututtuka da ake dauka daga ruwa.

Asusun ya kara da cewa, sama da yara miliyan 2.8 ne a yankin kahon Afirka da yankin Sahel ke fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, wanda hakan ke nufin suna cikin hadarin mutuwa daga cututtukan da ake dauka daga ruwa sau fiye da 11, idan aka kwatanta da yaran dake da wadatar abinci.

UNICEF ya ce, yana ba da agajin ceton rayuka da hidimomi na juriya a sassa daban-daban ga yara da iyalansu da ke fama da matsananciyar bukata a fadin yankin kahon Afirka da Sahel, amma kaso 3 cikin 100 ne kawai na kudaden da asusun ya nema game da inganta karfin iyalai na dogon lokaci a yankin kahon Afirka ya samu a halin yanzu. Yayin da ya samu kaso 22 cikin 100 na kudaden da ya nema, don biyan bukatun yara da iyalai masu rauni na samar da ruwa,da tsaftar muhalli, da shirye-shirye na tsafta a a yankin tsakiyar Sahel.

Russell ya ce, hanya daya tak da za a iya dakatar da wannan matsala, ita ce gwamnatoci,da masu ba da taimako, da kuma kasashen duniya, su kara kaimi wajen samar da kudade don biyan bukatun kananan yara, da ba da tallafi mai sauki na dogon lokaci don warware matsalar baki dayan ta. (Ibrahim)