logo

HAUSA

Sashen Raya Al’Adu Da Yawon Shakatawa Na Kasar Sin Na Kara Ingiza Bunkasuwar Tattalin Arzikin Kasar

2022-08-24 15:14:24 CMG HAUSA

DAGA CMG HAUSA

A yau Laraba 24 ga watan Agusta, sashen watsa bayanai na JKS, ya gudanar da taron manema labarai, inda a yayin taron aka bayyana cewa, tun bayan taron wakilan JKS karo na 18 da aka gudana yau shekaru 10 da suka gabata, sashen raya al’adu da yawon shakatawa na kasar Sin, ke kara ingiza bunkasuwar tattalin arzikin kasar. Kaza lika sashen ya zamo sabon karfi dake taka muhimmiyar rawa wajen ingiza sauye-sauye da daga matsayin tattalin arzikin kasar Sin, da kara kyautata nagarta, da biyan bukatun rayuwar al’ummar kasar.

Da yake karin haske game da hakan, babban darakta mai kula da ci gaban masana’antu, a ma’aikatar raya al’adu da yawon shakatawa ta Sin Miao Muyang ya ce, Sin ta kaddamar da sabbin matakai da dama, na bunkasa sashen raya al’adu da yawon shakatawa. Da farko, fannin masana’antun yana ta kara fadada, kana kasuwar fannin na kara samun tagomashi. Na biyu, ana kara samun fadadar hidimomin sashen, kuma dunkulewar sassan masana’antun bangaren na ingiza damar cin gajiya daga sashen. Na uku, kudaden jari da na hada hadar cinikayya a sashen na karuwa, yayin da ake kara samun manyan nasarori a cinikayyar waje ta fannin. Na hudu, gwamnati ta ci gaba da fadada matakan tallafawa fannin, ta yadda zai iya kaiwa ga jure mummunan tasirin annobar COVID-19.

A nasa bangare, mataimakin ministan ma’aikatar raya al’adu da yawon shakatawa Rao Quan ya ce, tun bayan taron wakilan JKS karo na 18 da aka gudana yau shekaru 10 da suka gabata, an ga babban tasirin gajiyar da aka samu daga fannin yawon shakatawar yankunan karkarar kasar Sin, wanda shi ma ya zama wani muhimmin bangare na farfadowar yankunan karkarar kasar. Karkashin wannan nasara, kauyuka kamar su Shibadong na lardin Hunan, da Huamao na yankin Zunyi a lardin Guizhou, sun cimma nasarar kawar da talauci da samun guraben ayyukan yi ta hanyar yawon bude ido.

Bisa wannan nasara ne ma, aka ayyana kauyukan Yucun na lardin Zhejiang, da kauyen Xidi na lardin Anhui, a matsayi na farko a duniya, ta fuskar yawon shakatawa na yankunan karkara, wanda hakan ya zamewa kasar Sin muhimmin abun alfahari da take gabatarwa duniya. (Saminu Alhassan)