logo

HAUSA

Jarin Sin ya taimaka wajen raya tsarin samar da kayayyaki a Afrika

2022-08-24 19:58:55 CMG Hausa

Majalisar kula da harkokin kasuwanci tsakanin Sin da Afrika (CABC), ta fitar da wani sabon rahoto kan jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen Afrika, wanda ya bayyana cewa, cikin shekaru 22 da suka gabata, bangarorin biyu sun samu dimbin nasarori ta kowacce fuska tare da hada gwiwa a bangarori da dama.

Rahoton da aka fitar a jiya, ya ce manyan jami’an majalisar sun ce kamfanonin kasar Sin sun yi kyakkyawan tasiri, kana sun kasance wani bangare mai matukar amfani na kasuwar Afrika. (Fa’iza Mustapha )