logo

HAUSA

Takaddamar Sin da Amurka ba za ta taimakawa gwamnatin Biden a yakin da take yi da hauhawar farashin kayayyaki ba

2022-08-23 14:22:39 CMG Hausa

Baamurke masanin tattalin arziki Jeffrey Sachs, ya ce takaddamar da Sin da Amurka ke yi game da wasu batutuwa na cinikayya da tattalin arziki, ba za ta taimakawa gwamnatin Joe Biden na Amurka ba, a yakin da take yi da hauhawar farashin kayayyaki.

Yayin zantawarsa da kafar CNBC cikin shirin tashar na "Street Signs Asia", Mr. Jeffrey Sachs, ya ce bai kamata gwamnatin shugaba Biden ta ci gaba da aiwatar da takunkuman da tsohuwar gwamnatin shugaba Trump ta kakabawa kasar Sin ba, la’akari da cewa, ga alamu na zahiri, shi ma shugaba Biden din na bin sahun manufofin muzgunawa kasar Sin, ko ma a ce yana aiwatar da manufofin sama da yadda tsohuwar gwamnatin ta Trump ta yi.

Farfesa Sachs ya ce “Ina ga wannan mataki ne mara kyau ga duniya baki daya. Mataki ne da ba zai warware kalubalen hauhawar farashi ba. Ga alama hauhawar farashi za ta tsawaita a Amurka, kuma maimakon daukar matakai na shawo kan ta, gwamnatin Amurka na aiwatar da matakan ingiza sabanin kasuwanci, ta hanyar kakaba takunkumai, da haifar da fito na fito a siyasar shiyyoyin duniya”.  (Saminu Alhassan)