logo

HAUSA

Tsarin tantance ingancin rigakafin Sin ya kai sabon mataki na nagarta

2022-08-23 21:22:32 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce tsarin tabbatar da ingancin rigakafi na kasar Sin ya kai wani sabon mataki na nagarta, kamar yadda tsarin tantance ingancin kayayyakin lafiya na kasashe na WHO ya bayyana.

Wannan na nufin kasar Sin na da tsayayyen tsarin sa ido mai inganci da zai tabbatar da nagarta da aminci da ingancin rigakafin da ta samar, ko ta fitar ketare. (Fa’iza)