logo

HAUSA

An sanya hannu kan yarjeniyoyin kasuwanci na biliyoyin kudade yayin baje kolin na’urorin zamani na Chongqing

2022-08-23 11:08:39 CMG Hausa

Rahotanni na cewa, an rattaba hannu kan manyan yarjejeniyoyin kasuwanci guda 7, wadanda suka kai darajar kudin Sin yuan biliyan 212.1, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 31.1, yayin baje kolin na’urorin zamani mai lakabin “Smart China Expo 2022”, wanda aka bude a ranar Litinin a birnin Chongqing, na kudu maso yammacin kasar Sin.

Yarjejeniyoyin kasuwancin dai sun kunshi fannonin samar da ababen hawa dake amfani da na’urori masu kwakwalwa, da fasahohin samar da manhajojin fasahar sadarwa, da fasahohin kirkire-kirkire, da amfani da na’urori wajen sarrafa kayayyakin masana’antu. Ana kuma fatan yarjejeniyoyin za su ingiza karfin birnin Chongqing, na cin gajiyar fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama.

Mashirya baje kolin sun ce, dandalin ya mayar da hankali ga mayar da birnin Chongqing wuri da zai bunkasa fasahohin tattara manyan bayanai, da zurfafa hadin gwiwa tare da manyan kamfanonin cikin gida da na waje. Cikin manyan yarjejeniyoyin kasuwanci da aka sanyawa hannu, akwai guda 54 na kudin Sin yuan biliyan 1 ko wannen su.

Taken baje kolin shi ne "Fasahohin zamani: karfafa tattalin arziki, kyautata rayuwa". Za a shafe yini 3 ana baje kolin, mai kunshe da ayyuka daban daban, ciki har da tarukan tattaunawa 20, yayin da za a gabatar da bayanai 120 game da wasu sabbin hajoji da fasahohi. Kaza lika za a gudanar da gasanni 10 masu nasaba da baje kolin. (Saminu Alhassan)