logo

HAUSA

Sin: Ya Kamata A Girmama Ikon Mulkin Kasa Da Cikakkun Yankunan Kasa Yayin Da Kasashen Duniya Suke Mu’amala Da Juna

2022-08-23 11:13:05 CMG Hausa

Kwamitin sulhu na MDD ya shirya wani taro dangane da inganta yin shawarwari da hadin gwiwa a kokarin tabbatar tsaro na bai daya a jiya Litinin bisa shawarar kasar Sin, wadda ke shugabantar kwamitin sulhu a wannan wata, inda Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya shugabanci taron.

Zhang Jun ya nuna cewa, girmama ikon mulkin kasa da cikakkun yankunan ta, wadda aka tanada cikin kundin tsarin MDD, babban tushe ne na dokokin kasa da kasa na zamanin yanzu, da kuma hulda a tsakanin kasa da kasa. Ya ce idan an kau da kai daga wannan muhimmiyar ka’ida, to, za a hambarar da baki dayan tsarin dokokin kasa da kasa, za a jefa duniyarmu baki daya cikin lokacin duhu, kuma ba za a iya tabbatar da tsaron kowa ba. Don haka dole ne a fito fili wajen tsayawa kan girmama ikon mulkin kasa, da cikakkun yankunan kasa, da hanyar raya kasa da tsarin zamantakewar al’ummar kasa, wadda jama’ar wata kasa suka zaba da kansu, da kokarin da kasashen duniya suke yi domin kiyaye dinkuwar kasa, da hadin kan al’ummomi. Wannan ita ce muhimmiyar ka’idar raya hulda a tsakanin kasa da kasa. Haka kuma, babban tushe ne na tabbatar da tsaro na bai daya.

Jami’in ya kara da cewa, har kullum kasar Sin na girmama ikon mulkin kasa, da cikakkun yankunan kasashen duniya. Tana kuma mutunta gaskiya da adalci a duniya. Kana tana goyon bayan kokarin da kasashen duniya suke yi wajen kiyaye tsaron bai daya. Har ila yau, kasar Sin za ta dauki dukkan matakai, na kiyaye ikon mulkin kanta, da cikakkun yankunanta. (Tasallah Yuan)