logo

HAUSA

Girmama cikakken ’yanci da yankunan kasa, wajibi ne a kan kowacce kasa babba, ko karama

2022-08-23 19:38:25 CMG Hausa

A matsayinta na shugabar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a wannan wata, kasar Sin, bisa jagorancin wakilinta na dindindin, ta kira taro kan samar da tsarin tsaro da ya dace da yanayin da ake ciki da girmama cikakken ’yanci da yankunan dukkan kasashe, domin samun yanayin tsaro mai karko a duniya.

Hakika kiran wannan taron da Wakilin Sin Zhang Jun ya yi ta zo a daidai lokacin da ya dace, ganin yanayin kalubale da duniya take ciki da kuma yadda ake keta cikakken ’yancin kasashe da takalar fada da kuma ingiza tayar da rikici.

Zamanin mulkin mallaka da danniya ko cinikin bayi ya wuce. Ana cikin wani sabon zamani da ake neman ci gaba ta hanyar girmamawa da moriyar juna. Akwai bukatar kasashen da suke ganin su shafaffu da mai ne, su dai na kokarin dawo da hannun agogo baya, domin duniya ta ci gaba. Girmama cikakken ’yancin kasa ya zama wajibi a kan kowacce kasa babba, ko karama.

Kasashen duniya da al’ummominsu sun bambanta, suka san yanayin da suke ciki da manufofi mafi dacewa da su, kuma su kadai ne za su san yadda ya kamata su shawo kan matsalolin dake addabarsu. Don haka, bai kamata a rika nunawa kasashe fin karfi kan harkokinsu na gida ba, ko kuma a rika nuna musu an fi su sanin abun da ya fi dacewa da su ba.

Kamar yadda Zhang Jun ya bayyana yayin taron, dole ne a samu bambancin ra’ayi daga kasa da kasa kan batutuwan tsaro, amma ya kamata a samu daidaito ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa.

Shirin tsaron duniya da shugaban kasar Sin ya gabatar ga taron BOAO a watan Afrilu, ya gabatar da wata alkibla ta cimma tsaro na bai daya tare da warware matsaloli masu masu ruwa da tsaki. An riga an san kasar Sin ba mai kaunar rikici ba ce, domin an ji, kuma an ga yadda al’ummominta da suka kunshi kabilu daban daban ke rayuwa cikin jituwa da zaman lafiya, don haka duk wani shiri da za ta gabatar don gane da hakan, a ganina abu ne da ya kamata a karba da hannu bibbiyu, tun da burinta shi ne, gina duniya mai kyakkaywar makoma cike da tsaro da kwanciyar hankali. Akwai bukatar sauran kasashen duniya su mara mata baya, kuma su ma su yunkura, su hada karfi da karfi wajen ganin an samu ci gaban duniya da kwanciyar hankali, ta hanyar hakuri da girmama juna da tabbatar da adalci. (Fa'iza Mustapha)