logo

HAUSA

Sin na maida hankali ga tattaunawa game da shiga yarjejeniyar DEPA

2022-08-23 11:36:16 CMG Hausa

Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta ce, Sin din na maida hankali matuka ga tattaunawa, don gane da nufinta na shiga yarjejeniyar hadin gwiwa, ta raya tattalin arziki mai nasaba da fasahar sadarwa ko DEPA a takaice.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar, ta biyo bayan wallafa ayyukan bangaren Sin, wanda ya shafi shirin kasar na amincewa da yarjejeniyar ta shiyya, irinta ta farko mai alaka da raya tattalin arziki ta fasahar sadarwa.

Kasashen New Zealand, da Singapore da Chile ne suka kaddamar da yarjejeniyar DEPA a watan Mayun shekarar 2019, aka kuma sanya mata hannu a watan Yunin shekarar 2020. Kaza lika yarjejeniyar na kushe da tsare-tsare, da manufofi na raya fannin tattalin arziki mai nasaba da fasahar sadarwa. Ita ce kuma irinta ta farko da wata shiyya ta tsara a duniya baki daya.

DEPA ta karade kusan dukkanin sassan raya tattalin arziki mai nasaba da fasahar sadarwa, tun daga ingiza hada-hadar cinikayya, zuwa fannin tsaron bayanan daidaikun mutane. Kuma a watan Nuwambar bara ne kasar Sin ta gabatar da bukatar shiga yarjejeniyar.

A matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, Sin na gaggauta raya fannin tattalin arziki mai nasaba da fasahar sadarwa, da fadada damar hukumominta, na shiga a dama da su a fannonin tsara dokoki da ka’idoji da sharudda.

A fannin ci gaban sashen kuwa, Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran kasashe, wajen kyautata muhallin cudanya, da raba moriya, da kara ba da gudummawa, kamar dai yadda ma’aikatar kasuwancin ta Sin ta bayyana.  (Saminu Alhassan)