logo

HAUSA

Sin ta yi tir da ziyarar da mamban majalisar dokokin Japan ya kai yankin Taiwan

2022-08-23 20:31:12 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana a yau cewa, ziyarar da mamban majalisar dokokin kasar Japan ya kai Taiwan ta hanyar yin watsi da korafin kasar Sin, katsalandan ne cikin harkokin gidanta.

Jami’in ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayar wani dan jarida game da ziyarar da mamban majalisar dokokin Japan, ya kai yankin Taiwan.

A cewarsa, ziyarar ta keta manufar kasar Sin daya tilo a duniya, da kuma daftarorin yarjejeniyoyi 4 da Sin da Japan suka cimma, haka kuma ya aike da wani sako na kuskure ga masu neman ‘yancin kan Taiwan.

Ya ce kasar Sin na tir da abun da dan majalisar ya aikata, kuma za ta dauki matakan martani domin kare cikakken ‘yancinta da ikon mallakar yankunanta. (Fa’iza Mustapha)