logo

HAUSA

Hidimar yanar gizo na bunkasa farfadowar yankunan karkarar kasar Sin

2022-08-23 11:07:29 CMG Hausa

Saurin fadadar hidimomin yanar gizo ko intanet, a sassan yankunan karkarar kasar Sin, tun bayan babban taron JKS karo na 18 da ya gudana a shekarar 2012, ya ci gaba da bunkasa farfadowar yankunan karkarar kasar. Cikin shekaru 10 da suka gabata, al’ummun yankunan karkarar kasar, na more hidimar yanar gizo mai sauri da inganci, wadda ke sada su da sauran sassan duniya.

Ya zuwa shekarar 2021, fadadar hidimar yanar gizo a sassan karkarar kasar Sin ya kai kaso 57.6 bisa dari, adadin da ya dara na shekarar 2012 da kaso 33.9 bisa dari. Kaza lika a tsakanin wannan lokaci, adadin iyalai dake kan manyan turakun sadarwa na yanar gizo a kasar ya karu, daga miliyan 40.76 zuwa miliyan 157.7, karin da ya kai na kaso 287 bisa dari. Kari kan hakan, saurin yanar gizo da ake amfani da ita a yankunan karkarar kasar, na yin kunnen doki da na yankunan birane.

A daya hannun kuma, yawan kudaden shiga daga sayayya ta yanar gizo, na kayayyakin da ake sarrafawa a yankunan karkarar kasar ta Sin, shi ma ya karu, daga darajar kudin kasar yuan biliyan 353 a shekarar 2015, zuwa yuan tiriliyan 2.05 a shekarar 2021.

A yanzu haka, makarantun firamare da na midil dake sassan kasar Sin, na amfani da intanet mai saurin gaske, inda daliban dake yankunan karkara ke iya cudanya da malamai da sauran daliban dake yankunan birane, tare da daukar darussa ba tare da shiga aji ba.

Bugu da kari, hidimar kiwon lafiya ta hanyar amfani da yanar gizo, ta karade sama da kaso 90 bisa dari na gundumomin kasar Sin, bayan da aka samar da na’urorin dake tallafawa samar da hidimar yanar gizo mai inganci.

Samar da ababen more rayuwa na fasahar sadarwa, na ci gaba da gaggauta rage gibin dake akwai, tsakanin yankunan karkara da na biranen kasar Sin, tare da samar da damar tura sakwanni kai tsaye, da kasuwanci ta yanar gizo, da inganta fasahohin noma, da kiwon lafiya ta yanar gizo, da sauran hidimomin zamani na raya karkara.  (Saminu Alhassan)