logo

HAUSA

Amurka ta aika da karin man da ta sace daga arewa maso yammacin Syria zuwa sansanoninta dake Iraki

2022-08-22 10:57:49 CMG Hausa

 

Kamfanin dillancin labaran kasar Syria (SANA) ya ba da rahoton cewa, sojojin Amurka sun aike da tankokin mai 137 makare da man da suka sata daga rijiyoyin mai dake yankin arewa maso gabashin kasar zuwa sansanoninsu da ke Iraki jiya Lahadi. Wannan shi ne man a baya-bayan nan da sojojin na Amurka suka sata da suka yi jigilarsa zuwa sansanin na Amurka dake kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran SANA ya ce, an aika tankokin man da aka yi jigilarsu na baya-bayan nan ne, cikin rukunoni biyu daga rijiyoyon mai na lardin Hasakah dake arewa maso gabashin kasar jiya da safe, tare da taimakon dakarun Kurdawa na Syrian Democratic Forces(SDF).

Da wannan man na baya-bayan da sojojin suka sata, Amurka ta kwashe jimillar tankoki 535 na man kasar Syria da ta sace, tun daga ranar 11 ga watan Agusta zuwa yanzu. Gwamnatin Syria dai ta zargi Amurka da satar albarkatun kasar, kamar mai, da gas, da kuma alkama.

A ranar 8 ga watan Agusta, ma'aikatar man fetur ta Syria ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, Amurka da sojojinta na haya, suna sace kusan ganga dubu 66 na mai a kowace rana a Syria, kusan kashi 80 cikin 100 na man da ake hakowa a kasar.

Sanarwar ta kara da cewa, rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a kasar, ya janyowa masana'antar man kasar hasarar da ta kai dalar Amurka biliyan 105. (Ibrahim)