logo

HAUSA

Minista: mahukuntan Najeriya sun zafafa yakar kungiyoyin da ke dauke da makamai ba bisa ka'ida ba

2022-08-22 10:44:13 CMG Hausa

 

Ministan tsaron Najeriya Bashir Magashi ya bayyana cewa, rundunar sojojin kasar ta kara kaimi, wajen murkushe masu tsattsauran ra'ayi da kungiyoyin 'yan fashi da makami don magance matsalar tsaro a kasar.

Magashi ya bayyana hakan ne Asabar din da ta gabata a Abuja, babban birnin kasar. Yana mai cewa, sojoji da sauran jami’an tsaro, sun ba da karfi da karfe domin fatattakar ‘yan ta’adda daga maboyarsu.

Ya kara da cewa, an baza jami’an tsaro zuwa manyan titunan kasar da ke fama da matsalar satar mutane, gami da yankunan arewa ta tsakiya da arewa maso yammancin kasar, domin zakulo ‘yan bindigar da ke boye a dazuka. Ya zuwa yanzu jami’an tsaron, sun yi nasarar lalata sansanonin ‘yan bindiga da dama tare da kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.

Ministan ya ce, sama da ‘yan bindiga 70,000 da iyalansu ne suka mika wuya ga sojoji a ‘yan watannin nan, kuma dubban mutanen da suka rasa matsugunansu sun koma gida.

A kudancin Najeriya ma, sojoji suna fafatawa don dakile haramtacciyar kungiyar nan dake fafutukar neman kafa kasar Biafra da kuma dakile manyan laifuka kamar satar danyen mai da fasa bututun mai.(Ibrahim)