logo

HAUSA

Guterres: Dole ne a shigar da takin zamani da amfanin gona na Rasha cikin kasuwar duniya lami lafiya

2022-08-21 16:09:13 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya ce dole ne a shigar da takin zamani da amfanin gona na kasar Rasha cikin kasuwar kasa da kasa lami lafiya, in ba haka ba, za a iya gamuwa da matsalar karancin hatsi a shekara mai zuwa.

Antonio Guterres ya yi rangadi a cibiyar sulhu kan jigilar hatsi zuwa ketare ta Black Sea dake birnin Istambul na kasar Turkiye a jiya, kuma ya ziyarci birnin Odessa dake kudancin kasar Ukraine a shekaran jiya, inda ya shaidawa wa manema labarai cewa, yarjejeniyoyi a jere da aka daddale, sun hada da yadda za a shigar da abinci da takin zamani na Rasha cikin kasuwar kasa da kasa lami lafiya, yana mai cewa idan aka gaza samun isasshen takin zamani a bana, to za a gamu da matsalar karancin hatsi a shekarar 2023, don haka, abu ne mai muhimmnaci matuka a fitar da karin abinci da takin zamani daga kasashen Ukraine da Rasha.

A ranar 22 ga watan Yulin bana ne Rasha da Ukraine tare da MDD da Turkiye, suka daddale yarjejeniya game da farfado da jigilar amfanin gona a tashar ruwan tekun Black Sea, inda aka bayyana cewa, za a kafa cibiyar sulhu domin tabbatar da jigilar hatsi cikin lumana. Rasha da Ukraine kuma, sun yi alkawari cewa, ba za su kai hari kan jiragen ruwan jigilar amfanin gona ba. (Jamila)