logo

HAUSA

Bloomberg: Fiye da rabin kamfanonin Amurka za su rage ma'aikata

2022-08-20 16:53:25 CMG Hausa

 

          

Kafar watsa labarai ta Bloomberg ta bayar da rahoton cewa, wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa, fiye da rabin kamfanonin Amurka baki daya, suna shirin korar ma'aikata.

Binciken, wanda ya shafi fiye da shugabanni da mambobi 700 na hukumar darektocin masana’antu daban-daban, ya gano rabin wadanda aka tattauna da su, matsalar ta shafe su, kuma kashi 52 cikin 100 sun aiwatar da shirin dakatar da daukar ma’aikata.

Rahoton ya ce, kora da dakatar da daukar ma’aikata, na kara yawa a Amurka, kuma manyan kamfanoni da suka hada da Walmart da Apple da Oracle, sun sanar da rage yawan ma’aikatansu a ‘yan makonnin nan.(Ibrahim)