logo

HAUSA

Wang Yi ya zanta da mai baiwa shugaban Faransa shawara kan harkokin wajen kasar ta wayar tarho

2022-08-20 16:50:53 CMG Hausa

A jiya ne, memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya tattauna ta wayar tarho da mai baiwa shugaban kasar Faransa shawara kan harkokin waje Emmanuel Bonne.

Wang Yi ya bayyana cewa, Sin da Faransa manyan kasashe ne dake da ‘yanci, yayin da suke tinkarar yanayin duniya mai sarkakkiya, ya kamata su kara daukar alhakin dake wuyansu na tabbatar da zaman lafiya a duniya da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare.

Wang Yi ya yi bayani game da matsayin Sin kan batun Taiwan, kana ya yabawa kasar Faransa kan yadda take tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, kana ya jaddada cewa, kasar Amurka da ‘yan aware na yankin Taiwan, suna yunkurin lalata yanayin da ake ciki a yankin Taiwan da saba wa ka’idar Sin daya tak a duniya, kuma hakan zai kawo babbar illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan.

A nasa bangare, Bonne ya bayyana cewa, kasar Faransa ta amince da ka’idojin kiyaye dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankili a yankuna, ra’ayin Faransa ya yi daidai da na kasar Sin, wato tana adawa da ra’ayin yakin cacar baka, da nuna adawa da juna a tsakanin kungiyoyin kawancen kasa da kasa, kuma tana fatan yin kokari tare da kasar Sin wajen tinkarar rikicin kasa da kasa da yankuna don nuna wa duniya ra’ayin hadin gwiwa da juna. Ya kara da cewa, a koda yaushe Faransa tana bin manufar Sin daya tak a duniya, kuma matsayinta game da girmama ikon mulkin kasa da cikakkun yankunan kasar Sin bai taba sauyawa ba. (Zainab)