logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Cimma Manyan Nasarori A Fannin Gina Intanet A Cikin Shekaru 10 Da Suka Gabata

2022-08-20 16:06:42 CMG Hausa

A matsayinta na kasar dake kan gaba wajen yawan masu amfani da intanet a fadin duniya, kasar Sin na kan hanyar sauyawa daga yawan adadi zuwa raya harkar intanet mai inganci.

A cikin shekaru goma da suka gabata, kasar ta cimma manyan nasarori wajen gina tsarin tafiyar da yanar gizo mai cike da tsaro, sakamakon kyautatuwar ababen more rayuwa masu inganci, da ci gaban fasaha da bunkasar tattalin arziki na zamani.

Tsakanin shekarar 2012 zuwa ta 2021, adadin masu amfani da yanar gizo a kasar Sin, ya karu daga miliyan 564 zuwa fiye da biliyan 1.03, abin da ya sanya ta zama matsayi na daya a duniya. Kasar Sin ta samar da manyan hanyoyin sadarwa na 5G da layin fiber optic mafi girma a duniya.

Darajar tattalin arzikin zamani na kasar Sin, ta tashi daga kudin Sin RMB yuan tiriliyan 11 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 1.6 a shekarar 2012 zuwa yuan tiriliyan 45.5 a shekarar 2021, wanda ya sanya ta ci gaba da zama kasa ta biyu a duniya a cikin shekaru da dama a jere.

Yawan jimillar tattalin arzikin zamani a GDPn kasar, shi ma ya karu daga kashi 21.6 cikin 100 a shekarar 2012 zuwa kashi 39.8 cikin 100 a shekarar 2021. Hada-hadar cinikayyar Intanet ta kasar Sin da tsarin biyan kudi ta wayar salula, duk sun kasance a kan gaba a duniya.(Ibrahim)