logo

HAUSA

Martanin da Sin ta mayar game da ziyarar Pelosi zuwa Taiwan ya dace da doka

2022-08-19 19:53:54 CMG Hausa

 

A yayin taron manema labarai na yau da kullum da aka gudanar Jumma’ar nan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya sake karyata kalaman da jami'an Amurka suka yi, game da yadda kasar Sin ta nuna rashin jin dadinta kan haramtacciyar ziyarar da Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan na kasar Sin. Yana mai jaddada cewa, matakin da kasar Sin ta dauka kan tsokanar Amurka, abu ne mai ma'ana, dake bisa doron doka, kana ya samu fahimta mai kyau da goyon baya daga kasashen duniya.

Wang Wenbin ya nanata cewa, kudurin kasar Sin na kiyaye ikon mallakar kasa da cikakkun yankunanta, bai taba sauya ba, ta kuma shawarci bangaren Amurka da kada ya yi kuskuren raina wannan aniya.(Ibrahim).