logo

HAUSA

Wang Yi ya jagoranci taron manyan wakilai game da nazarin matakan aiwatar da manufofin taron ministocin FOCAC na 8

2022-08-19 13:26:36 CMG Hausa

Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya karbi bakuncin taron manyan wakilai, game da nazarin matakan aiwatar da manufofin taron ministocin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC karo na 8.

Wang Yi, wanda ya jagoranci taron na jiya Alhamis ta kafar bidiyo, ya ce

taron ministocin FOCAC da ya gudana a birnin Dakar na kasar Senegal a watan Nuwambar 2021, ya aza wani ginshiki mai karfi game da alakar Sin da kasashen nahiyar Afirka. Ya ce yayin bikin bude taron na Dakar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana burin kasarsa na yin aiki tare da kasashen Afirka wajen aiwatar da muhimman ayyuka 9, matakin da ya yi matukar samun karbuwa, a matsayin wanda zai bunkasa ci gaban kasashen Afirka, tare da daga matsayin hadin gwiwar sassan 2. 

Wang ya kara da cewa, Sin da kasashen Afirka sun yi aiki tare, wajen shawo kan wahalhalu da kalubale, suna kuma aiki kafada da kafada, wajen aiwatar da sakamakon taro na 8 na ministocin kasashen dandalin FOCAC.

Ya ce bayan taron, Sin da kasashen Afirka sun samu manyan nasarori, tare da samun moriya cikin gaggawa, a fannin shawo kan kalubalen karancin abinci, da magance annobar COVID-19, da bunkasa ci gaba mai dorewa, tare da ingiza zaman lafiya da daidaito.

Ministan wajen na Sin ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, tare da gabatar da wasu shawarwari na tabbatar da nasarar gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a sabon zamani.

Taron dai na wannan karo, ya samu halartar ministoci daga kasashen Senegal, da jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Libya, da Angola, da Habasha, da Masar, da Afirka ta kudu, da kuma wasu karin wakilai daga hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU.

Har ila yau, taron ya amince da sanarwar manyan jami’an zaman, game da aiwatar da manufofin taron ministocin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC karo na 8. (Saminu Alhassan)