logo

HAUSA

Gobarar daji a arewacin Aljeriya ta haddasa mutuwar mutane 26

2022-08-18 12:19:08 CMG Hausa

Gobarar daji dake mamayar wasu wurare a arewacin kasar Aljeriya, ta haddassa mutuwar mutane 26 a jiya Laraba. Hukumar tsaron al’umma ta Aljeriya ta ce, jihohin kasar guda 14 ne suka sanar da bazuwar gobarar dajin har sau 39.

Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune, ya gabatar da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu sanadiyyar gobarar, ya kuma yi fatan samun sauki cikin sauri ga wadanda suka jikkata. Ya ce, gwamnatin kasar za ta hada dukkan rundunoni don shawo kan gobarar, da kuma jinyar masu jin raunuka.

A kwanan nan Aljeriya ta sha fama da yanayin tsananin zafi, tun daga farkon watan Agusta, kuma hakan ya haddasa tashin gobarar daji har sau 106, wadanda suka lalata dajin da fadin ya kai fiye da kadada 2500.

A watan Agusta na shekarar 2021 ma, gobarar daji da ta tashi a yankin arewacin Aljeriya, ta jikkata mutane da dama, baya ga wadanda suka rasu sakamakon hakan.  (Safiyah Ma)