logo

HAUSA

Rasha ta bukaci Amurka ta baiwa manyan jami’an gwamnatin kasar biza don halartar babban taron MDD

2022-08-18 10:23:16 CMG Hausa

Jakadan kasar Rasha dake Amurka Anatoly Antonov, ya bayyana a jiya Laraba cewa, ofishinsa ya riga ya bukaci Amurka da ta bayar da takardar izinin shiga kasa wato biza, ga ministan harkokin wajen Rasha, gami da ‘yan tawagar kasar, don su halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77, wanda za’a yi a watan Satumbar bana.

Anatoly Antonov ya bayyana cewa, Rasha ta nemi Amurka ta sauke nauyin dake wuyanta, a matsayinta na mazaunin hedikwatar MDD, ta bayar da takardar biza ba tare da bata lokaci ba, ga manyan jami’an gwamnatin Rasha.

Antonov ya kara da cewa, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba, Amurka tana kawo cikas ga ziyarar aikin jami’an kasar Rasha, ciki har da ziyararsu a MDD. Don haka Rasha ta bukaci Amurka da ta tabbatar da cewa, dukkan membobin tawagar kasar za su iya shiga cikin Amurka ba tare da wata matsala ba don halartar babban taron MDD.

Antonov ya kuma ce a yau Alhamis, zai sake zuwa ma’aikatar harkokin wajen Amurka, don bayyana ra’ayinsa game da harkokin bayar da biza ga tawagar ta Rasha. (Murtala Zhang)