logo

HAUSA

Ana shirin fadada layukan dogo na karkashin kasa dake birnin Beijing

2022-08-18 10:51:59 CMG Hausa

Mahukuntan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin sun bayyana shirin fadada layukan dogo na karkashin kasa dake birnin, zuwa tsayin kilomita 1,625 nan zuwa shekarar 2035.

A cewar hukumar tsara ayyuka da albarkatun kasar ta birnin, matakin fadada layin dogon na kunshe cikin shirin raya kasa na shekarar 2020 zuwa 2035, wanda a baya bayan nan gwamnatin birnin ta amince da shi.

A yanzu haka, layukan dogo na karkashin kasa dake cikin kwaryar birnin Beijing, na da tsayin kilomita 783, yayin da na wajen birnin suka kai tsayin kilomita 365.

Shirin bunkasa wannan fanni, ya kuma kunshi fadada sufurin jiragen karkashin kasa na birnin, ta yadda fannin zai kai kaso sama da 27 bisa dari, na jimillar sufurin ababen hawa a kwaryar birnin da kuma yankunan wajen sa.

Harkar sufurin jiragen karkashin kasa na birnin Beijing na da kyakkyawan tsarin kare lafiyar fasinjoji, da inganci da sauri, kana da yanayi na kare muhalli da kyautata tattalin arziki, ta fuskar rage cunkoson ababen hawa, da rage hayaki mai dumama yanayi.  (Saminu Alhassan)