logo

HAUSA

Antonio Guterres: Bai kamata a taba mantawa da wadanda suka fuskanci ayyukan ta’addanci ba

2022-08-18 10:50:14 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya ce, ko kadan bai kamata a taba mantawa da al’ummun da suka sha fama da ayyukan ta’addanci ba. Mr. Guterres ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, cikin sakonsa na bikin ranar tunawa da wadanda ayyukan ta’addanci suka rutsa da su, wanda ake gudanarwa a duk ranar 21 ga watan Agusta.

Babban jami’in na MDD ya ce, bikin na bana ya maida hankali ne ga muhimmancin waiwaye kan wannan batu, duba da yadda sau da dama wadanda hare-haren ta’addanci ke shafa kan ji tamkar an manta da su, jim kadan bayan aukuwar ibtila’in da ya auka musu. Don haka wajibi ne ga daukacin al’ummun duniya su rika waiwayen baya, tare da tunawa, da martaba wadanda ayyukan ta’addanci suka shafa.

Guterres ya ce, yana fatan jin bukatu, da kalubale, kai tsaye daga rukunin wadanda irin wannan ibtila’i ya shafa, yayin dandalin mutanen da ayyukan ta’addanci suka shafa, wanda zai gudana a wata mai zuwa.

A zaman babban taron MDD na shekarar 2017 ne aka kaddamar da wannan rana, wadda ake bikinta a duk ranar 21 ga watan Agusta, don tunawa da al’ummun da suka sha fama da ayyukan ta’addanci, da karrama wadanda suka tsira da ransu sakamakon hakan. (Saminu Alhassan)