logo

HAUSA

Xi yana rangadin aiki a birnin Jinzhou

2022-08-17 11:10:54 CMG Hausa

A yammancin jiya Talata, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya yi rangadin aiki a birnin Jinzhou na lardin Liaoning, inda ya je dakin tunawa da yakin Liaoshen, domin waiwayen tarihin ‘yantar da yankin arewa maso gabashin kasar, daga baya ya ziyarci lambun shan iska na tafkin gabas.

Yayin ziyararsa, Xi ya saurari rahotannin da aka gabatar game da yaki da ambaliyar ruwa, da kare muhallin halittu masu rai da marasa rai, inda kuma ya ba da muhimmin umurni. (Jamila)