logo

HAUSA

Kafofin watsa labarai na Siriya: Sojojin Amurka sun fitar da sabon kaso na mai da suka sata daga arewa maso gabashin kasar

2022-08-17 15:02:31 CMG Hausa


Bisa rahoton da kamfanin dillancin labarai na Siriya ya bayar a jiya Talata,cewar sojojin Amurka sun fitar da sabon kaso na mai da suka sata daga arewa maso gabashin Siriya zuwa kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labarai na Siriya ya ce shaidu daga al’ummun yankin na cewa, sojojin Amurka sun yi amfani da motocin dakon mai kimanin 65, wajen sufurin man zuwa sansaninsu dake Iraki.

Kaza lika rahoton ya ce, a kwanan nan yawan motoci masu dakon mai na sojojin Amurka da aka yi amfani da su wajen jigilar mai da suka sata daga Siriya zuwa Iraki sun kai 398.  (Safiyfah Ma)