logo

HAUSA

Sin Na Fatan Bangaren Amurka Zai Aiwatar Da Manufar Sin Daya Tak A Duniya

2022-08-17 19:31:58 CMG Hausa

Ranar 17 ga watan Agusta ne, aka cika shekaru 40 da kasashen Sin da Amurka suka ba da sanarwar hadin gwiwa dangane da sayar da makaman Amurka ga yankin Taiwan. A wannan rana, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, yana fatan bangaren Amurka zai yi amfani da kwarewa da darussan da ya koya a tarihi, ya kuma aiwatar da manufar kasar Sin daya tak a duniya bil hakki da gaskiya, kana ya dakatar da ci gaba da bin hanyar da ba ta dace ba, ta jirkita, ko tada zaune tsaye, game da ka'idar Sin daya tak a duniya.

Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, sanarwar da aka cimma a ranar 17 ga watan Agustan shekarar 1982, da sanarwar Shanghai, da sanarwar hadin gwiwar kulla huldar diflomasiya tsakanin Sin da Amurka, sun kasance tushen siyasa na dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma babban jigon su, shi ne manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Sai dai kuma, Amurka tana karya alkawuran da ta dauka, tana kuma ci gaba da nisanta kanta daga wannan ka'ida, wanda hakan ka iya haifar da babbar illa ga amincewa da juna a tsakanin kasashen biyu.

Wang ya jaddada cewa, idan har Amurka ta kiyaye manufar kasar Sin daya tak a duniya, hakika dangantakar dake tsakanin kasashen biyu za ta bunkasa cikin lumana, kana za a iya tabbatar da zaman lafiya a mashigin tekun Taiwan yadda ya kamata. Idan kuma aka keta wannan manufa, babu shakka dangantakar Sin da Amurka za ta fuskanci koma-baya, kuma halin da ake ciki a mashigin Taiwan zai fuskanci mummunan kalubale. (Ibrahim)