logo

HAUSA

An ayyana mataimakin shugaban kasar Kenya a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar

2022-08-16 10:35:17 CMG Hausa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Kenya, ta ayyana mataimakin shugaban kasar William Ruto, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Shugaban hukumar zaben Wafula Chebukati ya bayyana da yammacin jiya Litinin cewa, William Ruto ya samu kuri’u 7176,141 ko kuma kaso 50.49 na jimilar kuri’un da aka kada, inda ya doke shugaban bangaren hamayya Raila Odinga, wanda ya samu kuri’u 6942,930 ko kaso 48.85 na jimilar kuri’un.

Zanga-zanga ta barke a wasu sassan kasar nan take bayan sanar da sakamakon zaben, musamman a wuraren da magoya bayan Raila Odinga suka fi rinjaye a yammacin kasar da babban birnin Nairobi da kuma yankin gabashin kasar. (Fa’iza Mustapha)