logo

HAUSA

Xi Ya Aike Da Sakon Ta'aziyya Ga Takwaransa Na Masar Kan Gobarar Da Ta Tashi A Wata Majami’a A Masar

2022-08-16 20:22:19 CMG Hausa

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta'aziyya ga takwaransa na kasar Masar Abdel Fattah al Sisi, biyo bayan gobarar da ta tashi a wata majami’a a Masar.

Xi ya ce, ya firgita da samun labarin gobarar da ta tashi a wata majami’a a Masar, wadda ta yi sanadiyar asarar rayuka da dama. Kuma a madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin, da kuma shi kansa, ya mika sakon ta'aziyya ga wadanda lamarin ya shafa, tare da jajantawa iyalan wadanda suka rasu da wadanda suka jikkata, da kuma yiwa wadanda suka ji rauni fatan samun sauki cikin hanzari.(Ibrahim)