logo

HAUSA

Habasha ta kaddamar da babban titin da Sin ta gina a babban birnin kasar

2022-08-16 10:34:31 CMG Hausa

Gwamnatin Habasha ta kaddamar da wani babban titin da kasar Sin ta gina a Addis Ababa, babban birnin kasar.

Kamfanin China First Highway Engineering na kasar Sin ne ya gudanar da aikin titin, wanda ya fara daga shataletalen Alexander Puskin zuwa babban titin Gotera, mai tsawon kilomita 3.8 da ya kunshi sassa 3 da kuma ginin hanyar karkashin kasa mai hannu biyu, mai tsawon mita 320.

Magajiyar gari ta birnin Addis Ababa, Adanech Abiebie ta ce, aikin shaida ce ta jajircewar gwamnatin kasar wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba masu inganci cikin kankanin lokaci.

Ta kara da cewa, baya ga zama kyakkyawan misalin aiwatar da ginin titi a birnin da ma kasar, zai yi gagarumin taimako wajen kyautata zirga-zirgar ababen hawa a yankin mai matukar cunkoso.

A nasa bangaren, babban jami’in ofishin jakadancin Sin dake Habasha, Shen Qinmin ya ce, titin na shataletalen Alexander Puskin zuwa Gotera, alama ce ta hadin gwiwa da kawancen dake tsakanin Sin da Habasha. (Fa’iza Mustapha)