logo

HAUSA

Jirgin saman kasar Tanzania zai fadada jigila zuwa Nijeriya da Ghana

2022-08-16 10:33:39 CMG Hausa

Kamfanin jiragen sama na Air Tanzania (ATCL) mallakar gwamtain kasar, zai kaddamar da jigila zuwa Nijeriya da Ghana a badi, a wani yunkuri na fadada ayyukansa a fadin Afrika.

Manajan daraktan kamfanin ATCL, Ladislaus Matindi ya ce, jirgin zai kuma fara tashi zuwa biranen Goma da Kinshasa na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, tare da wasu yankuna a cikin gida.

Ladislaus Matindi ya ce, kamfanin ATCL na shirin inganta ayyukansa a kasar tare da kaddamar da zuwa sabbin wurare a nahiyar Afrika da ma sauran sassan duniya. Haka kuma, jirgin ya dawo da fara zirga zirga a Afrika ta kudu da kasar Sin, wadanda aka soke a baya saboda annobar COVID-19. (Fa’iza Mustapha)