logo

HAUSA

Wakilin Sin dake MDD ya yi kira da a gudanar da yarjejeniyar daina yaki ta Yemen a dukkan fannoni

2022-08-16 15:42:12 CMG Hausa

Wakilin Sin dake MDD Zhang Jun ya bayyana a gun taron harkokin Yemen da kwamitin sulhun MDD ya shirya, cewar kamata ya yi a aiwatar da yarjejeniyar dakatar da yaki ta Yemen daga dukkan fannoni, sannan a ci gaba da habaka sakamakon dakatar da yaki da kyautata yanayin jin kai da kuma halin da ake ciki a yankin.

Zhang Jun ya bayyana a yayin taron na jiya cewa, bayan aka dakatar da yaki a kasar Yemen, yawan fararen hula dake mutuwa ko jin rauni sakamakon ayyukan soja ya ragu sosai, amma wurare kamar Taiz da Marib da Shabwa ba su samu zaman lafiya ba, domin yanayin tsaro a wuraren babu inganci. Ya ce kamata ya yi bangarorin da abin ya shafa su aiwatar da yarjejeniyar dakatar da yaki a dukkan fannoni, da hana kowane hare-haren da ake kai wa fararen hula da tuntubar juna akai-akai ta hanyar amfani da tsarin kwamitin kula da harkokin soja, tare da warware matsaloli ta hanyar shawarwari.

Zhang Jun ya kara da cewa, bangaren Sin yana maraba da ganin gwamnatin Yemen ta samu ci gaba a kan harkokin musayar fursunonin da aka tsare tsakaninta da kungiyar Houthi. Yana kuma fatan bangarorin dake rikici da juna za su warware sabanin dake tsakaninsu a siyasance da karfafa shawarwari karkashin wakilin kula da harkokin Yemen na MDD, tare da cimma matsaya daya kan habaka yarjejeniyar dakatar da yaki. (Safiyah Ma)