logo

HAUSA

Sin: Cinikin Kayayyakin Abinci Zai Kara Amfanawa Jama'ar Sin Da Afirka

2022-08-16 20:04:21 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi wa taron manema labarai da aka saba gudanarwa Talatar nan karin haske, kan cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a fannin kayayyakin abinci. Yana mai cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali matuka kan karfafa hadin gwiwa a fannin aikin gona da Afirka, da kokarin kara shigo da kayayyakin amfanin gona daga kasashen Afirka.

Ya yi imanin cewa, tare da kokarin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, cinikayyar kayayyakin amfanin gona tsakanin Sin da Afirka za ta bunkasa, da samar da karin moriya ga jama'ar sassan biyu.

Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, kasar Sin ita ce kasa ta biyu mafi girma wajen sayen kayayyakin amfanin gona daga Afirka. A cikin 'yan shekarun nan, matsakaicin saurin karuwar yawan kayayyakin amfanin gona da Afirka ke fitarwa zuwa kasar Sin a duk shekara, ya kai kashi 11.4 bisa 100.

A shekarar 2021, yawan kayayyakin amfanin gona da kasar Sin ta sayi daga kasashen Afirka, ya karu da kashi 18.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2020. A yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) da aka gudanar a watan Nuwamban bara, kasar Sin ta ba da sanarwar kafa “hanyar shigar da kayayyakin amfanin gona daga Afirka”. Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta aiwatar tare da tsara hanyoyin da za a iya amfani da su, don saukaka hanyoyin shigar da kayayyakin amfanin gona daga Afirka, da ba da fifiko kan bukatun da kasashen Afirka suka yi don sayar kayayyakin amfanin gona a kasar Sin, da hanzarta aiwatar da hanyoyin shiga, da  tantancewa da kuma yin rajista. (Ibrahim)