logo

HAUSA

Annobar kyandar biri a duniya wani sakaci ne na gwamnatin Amurka

2022-08-16 11:35:07 CMG Hausa

Kafar yada labarai ta Truthout dake Amurka, ta ce sakacin gwamnatin Amurka ne ya haifar da kamarin da annobar Kyandar biri ta yi a duniya.

Rahoton da kafar yada labaran mai zaman kanta ta wallafa a shafinta na yanar gizo ya ce, sai da aka shafe watanni 3 bayan barkewar annobar a Amurka, kafin gwamnatin kasar ta ayyana ta a matsayin annobar dake bukatar daukin gaggawa.

Rahoton ya ce, da gwamnatin ta dauki mataki nan take cikin gaggawa, ta raba alluran riga kafi ga wadanda ke fuskantar barazana, watakila da cutar ba ta yi Kamari ba.

Ya kara da cewa, ana fuskantar matukar karancin riga kafin Jynneos, kana akwai karin fargaba tsakanin mutanen da cutar ta fi shafa a kasar.

Har ila yau, rahoton ya ce a wasu lokuta, sai mutane sun yi jiran sa’o’i a layi, sannan a ce musu riga kafin ya kare. (Fa’iza Mustapha)