logo

HAUSA

Rasha: A shirye take ta tattauna da Amurka kan musanyar mutanen kamar yadda aka tsara

2022-08-15 12:48:13 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana jiya Lahadi cewa, a shirye kasarta take ta tattauna da kasar Amurka kan batun musanyar mutane kamar yadda aka tsara, ta hanyar daukar hakikanan matakai.

Yayin da take tabo batun iyuwar musanyar ‘dan kasuwan Rasha Viktor Bout dake gidan yarin Amurka da aka tsara kafin karshen bana, Zakharova ta yi tsokaci cewa, ya dace a tattauna kan batun musanyar fursuna tsakanin kwararrun da abin ya shafa, kuma kasar Rasha ta riga ta shirya sosai kan tattaunar. Kuma tana fatan Amurka ba za ta sake yin cacar baki maras ma’ana ba.

Rahotanni na cewa, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya bayyana a ranar 27 ga watan Yuli cewa, Amurka ta riga ta gabatar da shawara ga Rasha, inda ta bukaci Rasha da ta saki ‘yar wasan kwallon kwandon na kasar Brittney Griner wadda ke tsare a gidan yarin Rasha bisa laifin fasa kwauri, da tsohon sojan ruwa Paul Whelan da kotun Rasha ta kama da laifin liken asiri. Daga baya a ranar 28 ga watan Yulin, Zakharova ta bayyana cewa, ya kamata a mai da hankali kan babbar moriyar sassan biyu yayin da suke tattaunawa. (Jamila)