logo

HAUSA

Sin ta kalubalanci Japan da ta yi watsi da ra’ayin nuna karfin soja

2022-08-15 21:00:35 CMG Hausa

A rana mai kamar ta yau wato 15 ga watan Agusta, shekaru 77 da suka wuce, rana ce da kasar Japan ta sanar da mika wuya ba tare da gindaya wani sharadi ba. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, yau shekaru 77 da suka wuce, al’ummar kasar Sin da na kasashen duniya, sun yi nasara kan maharan dake bin ra’ayin nuna karfin soja da ra’ayin danniya a yaki. Wannan babbar nasara, ta kasance a ko da yaushe a cikin tarihin tabbatar da adalci ga al'ummar kasar Sin da 'yan Adam baki daya.

Wang ya bukaci bangaren Japan da ya koyi darasi na tarihi da yin watsi da ra’ayi na ayyukan soja. (Zainab)