logo

HAUSA

Kasar Sin za ta dauki sabbin matakan martani dangane da ziyarar ’yan majalisar dokokin Amurka a Taiwan

2022-08-15 11:34:52 CMG Hausa

Kakakin ofishin jakadancin Sin a Amurka Liu Pengyu, ya ce kasarsa na adawa da duk wani nau’i na dangantakar diflomasiyya tsakanin Amurka da Taiwan, kuma za ta mayar da martani ga takalar Amurka.

Liu Pengyu ya bayyana haka ne a jiya, yayin da wasu ’yan majalisar wakilan Amurka daga jam’iyyun siyasa biyu na kasar suka nufi Taiwan.

A cewar kakakin, alhakin yanayin da ake ciki a zirin Taiwan na wuyan Amurka, kuma dole ne ta dauki nauyin duk abun da ziyarar da ’yan majalisar dokokin kasar suka kai Taiwan za ta haifar. Ya ce, har ila yau, ziyarar ta tabbatar da cewa Amurka ba ta burin ganin zaman lafiya a zirin Taiwan, kuma ba ta yin kasa a gwiwa wajen fito na fito da kasar Sin tare da tsoma baki cikin harkokin gidanta. (Fa’iza Mustapha)