logo

HAUSA

Masanan kasa da kasa: Ba za a yarda Japan ta musunta tarihin kai hari ba

2022-08-15 15:22:47 CMG Hausa

Kasar Japan ta sanar da mika wuya ba tare da gindaya sharadi ba a ranar 15 ga watan Agustan shekarar 1945, amma wasu ‘yan kasar sun musunta tarihin kasar na kai hari, kan wannan batu, masanan wasu kasashen Asiya sun bayyana cewa, ra’ayinsu yana da hadari, kuma ba zai yiwu a yarda ba.

Shahararren masanin dake aiki a kafar watsa labarai, ‘dan asalin kasar Malaysia dake rayuwa a kasar Singapore Zhong Tianxiang yana mai cewa, mutane da yawan gaske sun rasa rayuka sakamakon harin da sojojin kasar Japan suka kai yayin yakin duniya na biyu, wannan hakikanin abu ne na tarihi, wanda ba zai yiyu a musunta ba, musamman ma a kasashen Asiya. Kowace shekara mun saba da tunawa da alhinin wadanda suka rasu yayin yakin domin jaddada cewa, bai kamata a manta da tarihi ba. Idan Japan ta musunta tarihi, har ta gyara abubuwan da aka rubuta kan batun cikin litattafan daliban makarantar kasar, ba zai yiyu a yarda ba, saboda matakan da suka dauka aikata laifi ne. (Jamila)