logo

HAUSA

Jimilar kirin kayayyakin masarufi na zamantakewa a watan Yuli ta kai yuan triliyan 3.587

2022-08-15 14:50:38 CMG Hausa

A yau Litinin, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron ’yan jarida game da yanayin tattalin arzikin kasa, inda kakakin hukumar kididdiga ta kasar Sin, kana babban direktan sashen kula da aikin kididdigar tattalin arzikin kasar, Fu Linghui ya nuna cewa, jimilar kirin kayayyakin masarufi a watan Yuli ta kai yuan triliyan 3.587, wanda ya karu da 2.7% bisa makamancin lokacin a bara, kuma ya ragu da 0.4% bisa watan da ya gabata.

Ya bayyana cewa, a watan Yuli, yawan karuwar kudin da manyan masana’antu suka bayar, ya karu da 3.8% bisa lokaci na bara, wanda ya ragu da 0.1% bisa watan da ya gabata.(Safiyah Ma)