logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da kakakin shugaban Nijeriya

2022-08-14 15:49:54 CMG Hausa

A ranar 12 ga wannan wata ne, jakadan Sin dake kasar Nijeriya Cui Jianchun, ya gana da kakakin shugaban kasar Nijeriya kuma mai ba wa shugaban shawara kan harkokin watsa labaru da yada manufofin gwamnati Femi Adesina.

A yayin ganawar, jakada Cui ya bayyana cewa, Sin ta dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakanin Sin da Nijeriya, kuma tana son yin amfani da manufofin raya kasa na 5GIST don yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, a matsayin jagoran inganta hadin gwiwar bangarorin biyu a fannoni daban-daban, a kokarin samun hadin gwiwa mai inganci a tsakanin kasashen biyu.

Jakada Cui ya bayyana cewa, ziyarar baya-bayan nan da shugabar majalisar wakilan jama’ar Amurka ta kai yankin Taiwan na kasar Sin, ta saba wa “manufar Sin daya tak a duniya” da kuma hadaddiyar sanarwa guda uku da Sin da Amurka suka cimma, kuma ta kawo illa ga tushen siyasa kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, da keta ikon mulkin kan kasa da cikakkun yankunan kasar Sin, da kawo illa ga zaman lafiya a yankin Taiwan. Don haka Sin tana adawa da wannan batu, kuma za ta dauki kwararan matakai don tabbatar da kare martabar kasa da dinkuwar kasa baki daya.

A nasa bangare, Adesina ya bayyana cewa, shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, yana dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakanin Nijeriya da Sin, kuma ya yaba da irin taimakon da kasar Sin take baiwa Nijeriya a fannonin gina kayayyakin more rayuwa da sauransu. Ya yi imani da cewa, bisa jagorancin shugabannin kasashen biyu, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, a fannoni daban-daban, za ta ci gaba da samun ingantuwa. Bangaren Nijeriya ya tsaya tsayin daka wajen martaba “manufar Sin daya tak a duniya”. (Zainab)