logo

HAUSA

Xi Ya Amsa Wasikar Da Wasu Jarumai Suka Rubuta Masa

2022-08-14 15:11:28 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasikar da Li Peisheng da Hu Xiaochun, jarumai daga tushe dake aiki a wurin yawon shakatawa dake tsaunin Huangshan a lardin Anhui na gabashin kasar Sin suka rubuta masa, inda ya bayyana fatan za su ci gaba da gudanar da aikin da kuma kasance abin koyi

A cikin wasikar tasa, Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya yaba da kokarin Li da Hu suka dade suna bayarwa da himma wajen kiyaye tsaunin da kuma bishiyar Guest-Greeting Pine, wadda ta kasance alamar tsaunin na Huangshan.

Tun daga shekarar 2008, kasar Sin take ba wa jarumai daga tushe lambar yabo, a matsayin ’yan kasa na gari. Kuma Li da Hu sun shiga cikin jerin wadanda suka samu lambar yabon a shekarar 2012 da 2021, bi da bi. (Ibrahim)