logo

HAUSA

Mataimakiyar Firaministan Sin Ta Yi Kira Da A Gaggauta Dakile Barkewar COVID-19 A Hainan

2022-08-14 15:39:21 CMG Hausa

A jiya ne, mataimakiyar firaministan kasar Sin Sun Chunlan, ta yi kira da a gaggauta dakile cutar COVID-19 da ta sake bulla a lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.

Sun, wadda mamba ce a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ta bayyana hakan a lokacin da ta kai ziyarar aiki a birnin Sanya dake gabar teku a Hainan.

Ta kuma jaddada inganta tsarin bai daya da raba albarkatu a dukkan fadin lardin, tare da daukar kwararan matakai don kawo karshen bullar cutar tsakanin jama'a cikin kankanin lokaci.

Ta kuma yi kira da a yi kokarin hanzarta gina asibitocin wucin gadi, da inganta dukkan hanyoyin gwajin kwayar cutar, da karfafa rigakafi da dakile yaduwarta a matakin al'umma.

Sun ta lura da cewa, ya kamata a bayar da tabbacin hidima ga masu yawon bude ido da suka makale. Ta kuma umarci mahukuntan lardin, da su gudanar da matakan tantance yiwuwar fuskantar hadari yadda ya kamata, tare da aiwatar da matakan kariya da dakile yaduwar cutar. (Ibrahim)