logo

HAUSA

Jayati Ghosh: Manufofin kudi na Amurka suna haddasa hadari ga sauran kasashe

2022-08-14 16:37:57 CMG Hausa

Jayati Ghosh, farfesa a fannin tattalin arziki a jami’ar UMASS Amherst ta kasar Amurka, ta bayyana wa ‘yan jarida a kwanakin baya cewa, manufofin kudi na tsuke bakin aljihu da baitulmalin kasar Amurka ya fitar, suna haddasa hadari ga sauran kasashe, kana ba za su iya tabbatar da warware matsalar hauhawar farashin kaya da kasar Amurka take fuskanta ba.

Ghosh ta bayyana cewa, tsauraran manufofin kudin na baitulmalin Amurka, za su haddasa janye jari daga kasashe masu tasowa da kwarara zuwa kasar Amurka, hakan zai haddasa rikicin basussuka da hadarin rikicin musayar kudi a yankuna da dama na duniya.

Ta kara da cewa, a halin yanzu, kasashe masu tasowa da dama ba su farfado daga cutar COVID-19 ba, kana suna fuskantar matsin lamban raguwar saurin bunkasuwar tattalin arziki, kuma matakan kara kudin ruwa da baitulmalin kasar Amurka ya dauka, za su tsananta matsalolin hauhawar farashin kaya a wadannan kasashe. A halin yanzu, farashin abinci da mai ya tashi a kasashe masu tasowa da dama.

Ghosh ta yi imanin cewa, a cikin goman shekaru da suka gabata, kasar Amurka ta kasance tana yin amfani da ikon musamman na kudin dala a matsayin kudin ajiye na duniya don buga kudin ba bisa ka’ida ba, ko kuma sanya takunkumi kan wasu kasashe ba bisa dokokin duniya ba, wadannan ayyuka sun zubar da kimar kasar Amurka a idon duniya. (Zainab)