logo

HAUSA

Shugaban Saliyo ya zargi masu zanga zanga da yunkurin kifar da gwamnati

2022-08-13 16:50:25 CMG Hausa

Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio, ya zargi masu zanga zanga da yunkurin kifar da gwamnatinsa. Maada Bio, wanda ya bayyana hakan a jiya Juma’a, ya ce tarzomar da ta barke, ta kuma yi sanadiyyar rasuwar ‘yan sanda 6, da a kalla fararen hula 21.

Shugaban na Saliyo, wanda ke tsokaci game da tarzomar, yayin jawabin da ya gabatarwa ‘yan kasar sa, ya ce ba tsadar kayayyakin masarufi mai nasaba da tabarbarewar yanayin tattalin arziki ce ta haifar da zanga zangar ba, illa dai kawai burin wasu na ganin bayan gwamnatin sa.

A ranar Laraba, ‘yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa, da bindigogi a wasu wuraren domin tarwatsa dandazon masu zanga zanga, wadanda suka rika jifa da duwatsu, tare da kona tayoyi a sassan birnin Freetown, da karin wasu garuruwan masu rinjayen ‘yan adawa dake tsakiyar arewacin kasar. (Saminu Alhassan)