logo

HAUSA

Hanyoyin jiragen kasa da Sin ta gina sun zama shaidar raya shirin “ziri daya da hanya daya”

2022-08-12 11:29:43 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, Sin tana kokarin gina layukan dogo a kasashen nahiyar Asiya, da Turai, da arewacin Amurka, da kuma Afirka, wadanda suka zama shaidun aikin raya shirin “ziri daya da hanya daya” da kuma hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wannan fanni.

Wang Wenbin ya bayyana yayin taron manema labarai na jiya cewa, hanyoyin jiragen kasa dake tsakanin Mombasa da Nairobi na kasar Kenya sun sa kaimi ga raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma da kuma kyautata zaman rayuwar jama’a a kasar Kenya. Shekaru biyar bayan fara zirga-zirgar jiragen kasa, yawan tikitin kujerun jiragen kasa da aka sayar ya zarce kashi 90 cikin dari. Kana bisa kididdigar da aka yi, yawan kudin da layukan dogo suka samu, ya zarce kashi 2 cikin dari bisa yawan GDP na kasar Kenya, kana sun samar da ayyukan yi kimanin dubu 50, tare da horar da kwararru fiye da 1700 a fannin ilmin hanyoyin jiragen kasa da sarrafa hanyoyin jiragen kasa a kasar Kenya.

Wani rahoton jaridar The Daily Telegraph ta kasar Birtaniya, ya sanya layin dogon dake tsakanin Mombasa da Nairobi a matsayin daya daga cikin manyan layukan dogo mafi samun karbuwa guda 13 a duniya. Kafar yawon shakatawa ta kamfanin dillancin labaru na CNN ya bada shawara ga masu yawon shakatawa kan muhimman abubuwa 20 da aka fi yi a kasar Kenya, inda hawa jirgin kasa tsakanin Mombasa da Nairobi ya kasance a matsayi na biyar. Kamar yadda shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa, layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi ya samar da kyakkyawar makoma ga dukkan mutanen kasar a fannonin samun ayyukan yi da wadata.

Wang Wenbin ya kara da cewa, wannan lamari na shaida cewa, ya kamata a yi hadin gwiwa da samun moriyar juna da adalci da wadata tare, wanda zai sa kaimi ga bunkasa dukkan sassan duniya baki daya. Ya ce Sin za ta ci gaba da kokari tare da bangarori daban daban don sa kaimi ga raya shirin “ziri daya da hanya daya” da bayar da gudummawa ga samun ci gaba da wadata na bai daya a duniya. (Zainab)