logo

HAUSA

Sin na goyon bayan kasashen Asia su hada hannu wajen inganta tsaro da hadin gwiwa da ci gaban nahiyar

2022-08-12 14:53:22 CMG HAUSA

 

Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya tattauna da kafafen yada labarai na kasar, bayan halartar jerin tarukan ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin gwiwa ta kasashen gabashin Asia, wato ASEAN a takaice.

Yayin tattaunawar da aka yi a jiya Alhamis, Wang Yi ya gabatar da muhimman nasarorin da aka cimma dangane da tarukan da aka yi tsakanin kasashen Sin da na ASEAN, tare da kuma bayyana kokarin da Sin take yi wajen inganta hadin kan yankin gabashin Asia.

A cewar Wang Yi, dukkan bangarori sun amince da bayar da muhimmanci ga musayar damarmakin samun ci gaga, da ’yancin bin addini da tsarin huldar kasa da kasa. Haka kuma ya ce, Sin na goyon bayan kungiyar ASEAN ta zama jigon hadin gwiwa a yankin, shawarar da kasashen ASEAN din suka yi maraba da ita. (Fa’iza Mustapha)