logo

HAUSA

Kasar Sin ta damu matuka da yanayin da tashar nukiliya ta Zaporizhzhia ke ciki

2022-08-12 10:30:14 CMG HAUSA

 

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun ya ce, kasarsa ta damu matuka da harin da ake kai wa tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia dake Ukraine.

Zhang Jun ya shaidawa taron kwamitin sulhu na majalisar cewa, kasarsa na kira ga bangarorin dake da ruwa da tsaki, da su kai zuciya nesa, tare da yin takatsantsan da kaucewa duk wani abu da zai yi tsaiko ga tsaron sinadaran nukiliya, kana kada su yi kasa a gwiwa wajen toshe kafofin samun hatsari.

A matsayinsa na shugaban kwamitin na watan Augusta, Zhang Jun ne ya jagoranci taron na jiya, wanda aka yi kan tashar Zaporizhzhia.

Da yake tsokaci a madadin kasarsa, bisa dogaro da bayanan da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta samu daga hukumar dake sa ido kan nukiliya ta Ukraine, wakilin na kasar Sin ya ce harin bai yi wata barazana ga tsaron sinadaran nukiliya ba, haka kuma matakin hasken makamashi mai illa da sinadaran ke fitarwa, bai dagu ba.

Sai dai ya kara da cewa, harin ya illata yanayin tashar na zahiri da tsarukan tsaronsa da na ma’aikata, har da yanayin samar da makamashi, abubuwan da suka tada hankalin al’ummun duniya. (Fa’iza Mustapha)