logo

HAUSA

Ziyarar da Pelosi ta kai Taiwan tamkar zagon kasa ce ga dimokradiyya

2022-08-12 20:20:20 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya musanta kalaman kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi game da yankin Taiwan, a taron manema labarai da aka saba gudanarwa a yau Jumma’a, inda ya nuna cewa matakin da Pelosi ta dauka na zuwa Taiwan, ba shi da wata alaka da dimokuradiyya, illa dai tauye tsarin dimokuradiyya, kuma hakan ya nuna yadda Amurka ta dora son kai sama da adalci na kasa da kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa, kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi, da wasu 'yan majalisar da suka halarci ziyarar yankin Asiya, sun gudanar da taron manema labarai a kwanan baya. Pelosi ta ce, wannan ziyara ta shafi dimokuradiyyar Taiwan, wadda ta dace da manufar kasancewar kasar Sin daya tilo ta gwamnatin Amurka, kuma ba ta neman sauya yanayin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan.

Game da haka, Wang Wenbin ya ce, kalaman Pelosi sun kara tabbatar da cewa, ziyarar da ta kai yankin Taiwan na kasar Sin, goyon baya ne da suka yi ga masu neman balle Taiwan daga kasar Sin.

Kasar Sin na da cikakken hakki, kuma ya zama wajibi ta dauki kwararan matakan mayar da martani kan tsokanar Amurka, bisa la’akari da kare mulkin kai da cikakken yankin kasa, da kiyaye ka'idar dangantakar kasa da kasa, ta rashin tsoma baki cikin harkokin gida, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan. (Mai fassara: Bilkisu Xin)