logo

HAUSA

Dole ne a hukunta kasar Amurka wadda ta fi keta hakkin dan Adam a duniya

2022-08-10 15:48:41 CMG Hausa

Kungiyar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin ta gabatar da wani rahoto a jiya Talata, inda ta gabatar da dimbin alkaluma da cikakken bayani game da laifukan keta hakkin dan Adam da kasar Amurka ta aikata a yankin gabas ta tsakiya da kewayensa, wadanda suka hada da ta da yake-yake, da aikata kisan kiyashi kan fararen hula, da saka takunkumi yadda ta ga dama, da neman haddasa rikici tsakanin al’ummomi, da dai sauransu. Wadannan al’amura sun shaida cewa, kasar Amurka ita ce wadda ta fi azabtar da Musulmai a duniya.

Kamar yadda aka wallafa cikin mujallar Smithsonian ta kasar Amurka, tun daga shekarar 2001 har zuwa yanzu, yake-yaken da kasar Amurka ta tayar, da matakan soja da kasar ta dauka, bisa fakewa da maganar yaki da ta’addanci, sun shafi kimanin kashi 40% na daukacin kasashen duniya, wadanda suka haddasa asarar rayukan mutane fiye da dubu 800. Cikinsu har da fararen hula wasu dubu 335.

Manyan laifukan da kasar Amurka ta aikata a yankin gabas ta tsakiya da sauran wuraren duniya, sun shaida yadda ta kasance mafi cin zarafin dan Adam, da neman yin babakere a duniya. Ban da haka, lamarin ya nuna cewa, “tsarin dimokuradiya na Amurka”, da “hakkin dan Adam irin na Amurka” yaudara ne kawai.

Kamata ya yi hukumar kare hakkin dan Adam ta majalisar dinkin duniya ta gaggauta aikin bincike kan aikace-aikacen kasar Amurka na keta hakkin dan Adam a yankin gabas na tsakiya, saboda ya zama dole a hukunta mai laifi. (Bello Wang)