logo

HAUSA

Wang Yi ya yi gargadi a fannoni uku game da sabon halin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan

2022-08-10 21:29:43 CMG Hausa

Memban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna da takwarorinsa na kasashen Mongoliya da Koriya ta Kudu, da Nepal a kwanan nan, inda ya sake jaddada matsayin gwamnatin kasarsa kan halin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan, yana mai jan kunnen jama’a game da wasu abubuwa masu hadari guda uku.

Na farko, a yi hattara cewa, Amurka za ta kara hura wutar rikici, da girke sojoji a wannan shiyya, da kara ta’azzara halin da ake ciki, don kirkiro sabuwar matsala.

Na biyu, a yi hattara cewa, masu yunkurin balle Taiwan daga kasar Sin za su ci gaba da hada baki da sauran wasu kasashe, don kara kawo baraka ga kasar Sin.

Na uku shi ne, a yi hattara cewa, ‘yan siyasar wasu kasashe za su jirkita gaskiya da gangan, domin neman cimma muradunsu a fannin siyasa.

Wang Yi ya ce, kasar Sin na fatan yin kokari tare da kasashe daban-daban, don kin yarda da duk wani yunkuri na tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, da nuna adawa ga duk wani yunkuri na lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan, da ci gaba da mutunta manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, a wani kokari na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan shiyya da ma duniya baki daya. (Murtala Zhang)