logo

HAUSA

Sin: dokar Amurka na gurgunta ayyukan ciniki na duniya

2022-08-10 11:01:05 CMG Hausa

Kungiyar raya harkokin ciniki ta kasar Sin da kungiyar ’yan kasuwan kasa da kasa ta kasar Sin sun sanar a yau Laraba cewa, doka mai alaka da na’urar lantarki ta Chip da sauran ayyukan kimiyya da fasaha da kasar Amurka ta gabatar, tana tare da burin habaka fifikon da kasar Amurka ke da shi a fannin samar da na’urorin lantarki na Chip, da cin zarafin sauran kasashe, ciki har da kasar Sin, ta fuskar mallakar fasahar samar da na’urar. Lamarin da zai tsananta takara, da hana farfadowar tattalin arzikin duniya, gami da yunkurin kirkiro sabbin fasahohi.

A cewar wadannan kungiyoyi na kasar Sin, kasar Amukra na amfani da karfinta wajen gurgunta ayyukan cudanya da hadin kai da ake gudanarwa tsakanin masu kula da masana’antu da ciniki na kasashe daban daban. Sa’an nan yadda kasar ta gabatar da sabuwar dokar zai haifar da mummunan tasiri kan aikin samar da kananan na’urori na Chip na kasashe daban daban, da kawo tsaiko ga ayyukan ciniki da zuba jari masu alaka da na’urar, batun da zai sabawa burin ’yan kasuwan kasashe daban daban na karfafa cudanya da hadin gwiwa tsakaninsu.

Saboda haka, kungiyar raya harkokin ciniki ta kasar Sin da kungiyar ’yan kasuwan kasa da kasa ta kasar Sin, sun bayyana kin amincewa ga dokar da kasar Amurka ta gabatar, tare da kira ga sassa daban daban na duniya da su dauki matakai don kokarin kawar da mummunan tasiri da dokar za ta haifar, gami da kare halaltattun hakokkinsu. (Bello Wang)